Hukumar Kare Hakkin Mai Saye da Amfani da Kayayyaki Ta Rufe Shago a Kano Saboda Sayar da Kayayyakin da Wa'adinsu Ya Kare.
Daga Hassan Mukhtar Abubakar A kokarinta na kare lafiya da dukiyoyin al'umma, Hukumar Kare Hakkin Mai Saye da Amfani da Kayayyaki ta jihar Kano (kano State Consumer Protection Council ) ta dauki matakin rufe wani shago da ke kan titin zuwa Gidan Zoo a birnin Kano. Sakataren zartarwar hukumar Alhaji zangina Jafaru shine ya bayyana hakan lokacin da ma'aikan hukumar tare da ma'aikan hukumar kwashe shara (REMASAB) suka ziyarci kan Titin Gidan Zoo. Alhaji zangina yace Wannan mataki na hukumar ya biyo bayan wani samamen da jami’anta suka kai, inda suka gano dimbin kayan da kudinsu yakai kimanin naira miliyan daya 1000000.wadanda wa’adin amfani da su ya wuce, abin da ke barazana ga lafiyar al'ummar jahar nan. Sakataren, ya ce rufe shagon wani bangare ne na kokarin tabbatar da cewa 'yan kasuwa suna bin ka’idojin da suka dace wajen sayar da kaya, musamman ma wadanda suka shafi abinci da lafiyar al'umma. Hukumar ta gargadi sauran 'yan kasuwa da su dub...