Gwamnatin Jahar Kano ta fitar da gargadin lafiya kan karatowar lokacin da aka fi fama da zazzabin Lassa zangon 2025/2026
Daga Muhammad Dayyabu Ali
Gwamnatin Jahar Kano ta hanyar Cibiyar dakile Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta fitar da cikakken gargadin lafiyar jama’a domin sanar da al’umma da masu ruwa da tsaki game da karatowar lokacin da aka fi fama da zazzabin Lassa zangon shekarar 2025/2026 a fadin Najeriya.
A cewar sanarwar da Darakta Janar na KNCDC, Dakta Muhammad Adamu Abbas ya sanyawa hannu a kai, wannan gargadi ya biyo bayan sanarwar da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayar kan yiwuwar karuwar yaduwar cutar Lassa tsakanin watan Oktoba zuwa Mayu, lokacin da ake yawan samun karin hadarin kamuwa da cututtuka.
Dakta Abbas ya bayyana cewa yanayin muhalli da tsarin rayuwa na Jihar Kano, musamman cunkoson jama’a, hanyoyin ajiya da tsaftar muhalli, na iya taimakawa wajen yaduwar kwayar cutar Lassa idan ba a dauki matakan kariya ba. Ya shawarci jama’a su kula da tsafta sosai, su ajiye abinci a cikin mazubi mai kyau da beraye ba za su iya shiga ba, su zubar da shara yadda ya dace, tare da kaucewa hulɗa da beraye ko najasarsu.
Ya jaddada cewa zazzabin Lassa ana iya kare kai daga gare shi kuma ana iya warkewa daga gare shi idan aka gano da wuri. Haka kuma ya bukaci ma’aikatan lafiya a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya su kasance cikin shiri, su rika bayar da rahoton gaggawa idan an samu wadanda ake zargin suna dauke da cutar, tare da bin ka’idojin kariya daga kamuwa da cututtuka.
Dakta Abbas ya kara da cewa a cikin shirin tsare-tsaren gaggawa da martani, Gwamnatin Jihar Kano ta sake bude Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) domin daidaita harkokin kai agaji, sa ido da kuma kula da wadanda ke dauke da cutar. Ya tabbatar da cewa cibiyar za ta ci gaba da aiki tare da abokan hulda da kungiyoyi masu ruwa da tsaki don tabbatar da saurin martani idan aka samu bullar cutar.
Haka kuma ya bukaci shugabannin al’umma, kafafen yada labarai, da kungiyoyin farar hula su taimaka wajen yada sakonni na fadakarwa kan kariya da rahoton gaggawa idan an samu alamun zazzabin Lassa.
Dakta Abbas ya tabbatar wa jama’ar Kano cewa gwamnati na ci gaba da ba da fifiko ga lafiyar al’umma, kuma za ta ci gaba da aiwatar da dukkan matakan kariya da martani yayin zangon wannan lokaci na zazzabin Lassa.
Comments
Post a Comment