Sunday, April 5, 2026

MARABA DA GWAMNAN KANAWA

Daga Farouk Musa Isa 

Shugaban Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano (#DMCSA) Pharmacist Gali Sule tare da dimbin magoya baya sun fito, kwansu da kwarkwata, don tarbar Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf  wanda ya dawo gida Jihar Kano daga Birni Tarayya Abuja, bayan da ya halarci Babban Taron Jam'iyyar #APC na Kasa.

A lokacin tarbar, Pharmacist Gali Sule da dubun-dubatar al'ummar Jihar Kano sun taru a Filin Tashi da Saukar Jiragen Sama na Malam Aminu Kano, yayin da aka yi dakon isowar Mai Girma Gwamna, wanda ya sauka da misalin karfe 2 da rabi na rana.


Sakamakon dandazon Kanawa masoya da suka yi fitar farin dango don yi wa Gwamna maraba da kuma nuna goyon bayansu gare shi, tawagarsa ba ta samu isa Gidan Gwamnati ba sai karfe 10 da 'yan mintuna na dare.

Wannan karamci da Kanawa suka nuna wa Gwamna Alh.Abba Kabir Yusuf manuniya ce da ke tabbatar da gamsuwa da irin ayyukan alheri da gwamnatin jiha ke malalawa a birni da kauyuka a karkashin tsarin nan na kishin jihar nan mai taken "Kano Farko', wato 'Kano First' a Turance.


A karkashin gwamnati mai ci, harkar lafiya ta inganta ta hanyar gina sababbin asibitoci da gyara wadanda ake da su, da samar da wadatattu kuma ingantattun magunguna, cikin farashi mai rahusa,  da kuma daukar ma'aikatan kula da lafiya.

Alal misali, nasararori da aka samu a Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jiha (DMCSA) kadai sun Isa abun tunkaho. A karkashin jagorancin Shugabanta Pharmacist Gali Sule, wannan hukuma ta biya bashi na Naira biliyan daya da milyan 172 (N1.172b). A karshen watan Disambar shekarar da ta gabata, wadatuwar magunguna a asibitoci (drug availability) ta karu da kaso 95 daga kaso 30. Haka kuma an samar da katafaren rumbun adana magunguna (Pharma-Grade Warehouse) wanda a baya babu irin sa a jihar Kano. An samar wa da hukumar jari mallakinta (operational fund value) na Naira miliyan 532, daga rashin jari na Naira miliyan 102 (N102m negative balance).

Baya ga bangaren lafiya, haka kuma an kyautata harkar ilimi. Haka zalika, ana ci gaba da samar da kayan more rayuwa (infrastructure), wadanda suka hada da tituna da gadoji da ruwan sha, da sauran su.

Haka abun yake idan aka leka bangaren noma, da kiwo, da sauran sassa.


Gwamna Abba Kabir Yusuf bai tsaya a iya manya-mayan ayyukan raya kasa ba (wato capital projects). Yana matukar bai wa jin dadi da walwalar jama’a muhimmanci ta hanyar gina dan Adam (ma'ana human development).

Daga cikin tsare-tsaren Gwamnatin Jihar Kano na gina dan Adam da kula da jin dadi da walwalar al'umma, ya zuwa yanzu (a wannan wata na Afirilu) Gwamna Yusuf ya biya hakokin 'yan fensho wanda ya kai Naira biliyan 32, daga cikin Naira  biliyan 48 da suke bi. Abun da ya rage bai wuce Naira biliyan 16 ba.

Har ila yau, gwamnati ta horar da matasa sana'o'i kala daban-daban, tare da ba su jari don dogaro da kai. Wannan kari ne a kan dubunnan matasa da aka dauka aiki a fanonni daban-daban.

Abun da Kanawa kawai suke jira shi ne, Allah Ya kai mu kakar zabe ta shekarar 2027, su nuna halacci, su saka alkhairi da alkhairi ta hanyar zazzagawa Gwamna, da ma jam'iyyar APC, kuri'u, daga kasa har sama.


No comments:

Post a Comment

Eid-el-Kabir: Pharm. Gali Sule Felicitates Gov. Yusuf, Muslim Ummah, Calls for Peaceful Coexistence

By Farouk Isa Musa  The Director General of Kano State Drugs and Medical Consumables Supply Agency (DMCSA), Pharm. Gali Sule, he...